Dafta Ibe Kachikwu

Daga Ibrahim Sulaiman

Haƙiƙanin dalilan da ya sa ƙaramin ministan man fetur Dafta Ibe Kachikwu ya kai ƙarar shugaban hukumar NNPC wato Dafta Maikanti Baru wajen Shugaba Muhammadu Buhari sun fito fili ƙarara.

A cikin wata takarda da ta yi ta walagigi a shafukan sada zumunta a ranar Talatar nan, ministan ya yi kira ga shugaban kasa da ya dau mataki akan Dafta Baru saboda zargin kauce ƙaida da rashin biyayya da ya ke yi masa da dai sauransu.

“Dole ne hukumomi  da shubannin hukumomin da ke ƙarƙashin wannan ma’aikata ta man fetur da su haɗe sahunsu wajen bin ƙa’idojin da wannan ma’aikata ta zayyana domin ciyar da ita gaba.

“Rashin yin hakan ko kuma ƙyale wasu su zama shafaffu da mai ka iya jawo naƙasu wajen cigaban ma’aikatar,” a cewar wasikar Dafta Kachikwu zuwa Shugaba Buhari.

Sai dai wani jigo da ya san ciki da wajen harkokin sha’anin mai, ya ce Dafta Kachikwu ba Dafta Baru ya fi jin haushi ba, illa Buhari da ya fi bawa Dafta Baru fuska.

“Haushin Kachikwu na farko shi ne Buhari ya fi sauraron Baru fiye da shi. Kuma Baru ya fi ministoci da yawa samun damar ganin shugaban kasa,” inji wannan mutum da ya ce a sakaye sunansa.

Wannan jigo ya kara da cewa Dafta Kachikwu bai so aka bada kwantiragin kawo iskar gas daga garin Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano ba.

A watan Mayun wannan shekaranne hukumar NNPC ta bawa kamfanin China Petroleum Group Engineering kwangilar shimfida bututun iskar gas din.

Wannan gagarumin aiki, wanda Shugaba Buhari ke matuƙar ƙauna, zai kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a arewacin ƙasar nan, kuma zai farfaɗo da masana’antun da su ka durƙushe a shiyyar.

“Duk zarge-zargen da ake yi wa Baru babu na almundahana ko rashawa da cin hanci. Kawai dai shi haushinsa akan kimar da Baru ke da ita a idon Buhari ne,” inji wannan jigo.

“Kachikwu babu kisisinar da bai yi ba akan kada Buhari ya naɗa Baru ya gaje shi. Idan Kachikwu na son mutuwarsa, to yana so Baru ya gaje shi a matsayin shugaban NNPC.”

LEAVE A REPLY