Ibrahim Magu

 

Hassan Y.A. Malik

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu, a lokacin da gidan talabijin na Channels ke tattaunawa da shi a wani shiri nasu mai suna Question Time, ya bayyana cewa sam rashin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC mai cikakken iko da majalisar dattijan Nijeriya ba ta yi ba, bai dada shi da kasa ba.

“Bana jin rashin tabbatar da ni a matsayin shugaban EFCC mai cikakken iko ya sauya yanayin yadda ‘yan Nijeriya suke kallona. Hasali ma dai, hakan wani kwarjini da kwarin giwa ya kara bani. Rashin tabbatar da ni din ya nuna ina gabatar da aikina yadda ya kamata ne kawai.”

“A yanayin aiki irin namu na yaki da cin hanci da rashawa, in kaga an gaggauta tabbatar da kai a matsayinka, to, hakan na nufin ba ka yin aikinka ne yadda ya kamata,” a cewar Magu.

Da aka tambaye shi me yasa shi ne wanda ya rike mukamin na farko da ya samu tsaiko wajen tabbatar da shi, sai Magu ya kada baki ya ce, “Wannan babu wata matsala ai! Watakila saboda akwai da dama cikin wadanda muke tuhuma a majalisa shi ne ya sa.”

“Sam wannan bai kawar da hankalina akan abubuwan da muke yi ba, sai ma dai karfin gwiwa da muka kara samu. Haka wata rana na ke tashi na ga jaridun kasar nan da munanan rahotanni game da ni, amma duk da haka gwiwarmu ba ta yi sanyi ba. Za mu ci gaba da fafutuka”

“Duk wadancan abubuwa ba za su dauke hankalina ba, babu wanda ya isa ya saye ni, kuma ba za mu fasa abubuwan da muke yi ba.”

LEAVE A REPLY