Wasu matasa masu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, sun yiwa mai neman takarar Shugaban kasa, kuma mawallafin jiradar kan intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore ihun bama yi a Kano.

Lamarin dai ya auku ne da misalin karfe 12 na rana, a fadar mai martaba Sarkin Kano, bayan da mai neman takarar Shugaban kasar, ya kaiwa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II caffa, a fadarsa.

Mawallafin Omoyele Sowore, ya kasance sahun gaba wajen sukar manufofin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda daga bisani ya ayyana aniyarsa ta neman takarar Shugaban kasa a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Wakilin Jaridar DAILY NIGERIAN da ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Kano, ya ruwaito cewar, matasan da suka yiwa Sowore ihun bama yi, sun yi basaja ne a zuwa sunje gaida Sarkin Kano, wannan ya sanya suka ci nasarar kutsa kai cikin harabar fadar, suna jiran fitowar Sowore.

Wakilinmu ya gano cewar, bayan da matasan suka ankare da motar da Sowore yake ciki, Marsandi C-Class ki1996, sai suka hau ihun bama yi suna daga kwalaye dake nuna adawa da zuwan Sowore Kano, da kuma nuna goyon bayansu ga Buhari.

Daga cikin kwalayen da matasan suka dinga dagawa suna cewar “Bama goyon bayan Sowore”, “Bama yi maka maraba da zuwa Kano Sowore”, “Tsarinka na nunawa Buhari kiyayya ba zai yi nasara ba” da sauran kalamai.

Haka kuma, wasu matasan na yin ihun “Bama yi, Sai Buhari”, yayin da wasu kuma ke daga kwalayen da suke dauke da rubutun da muka fada.

Wasu kuma sun matsa har kusa da motar dake dauke da Sowore inda suka rubuta “Sowore dole ka karanta sakonmu a gareka” Da sauran maganganu.

A lokacin da abubuwa suka nemi cakudewa, mai tuka motar da Sowore yake ciki, ya kara mata giya, inda ya fice a sukwane.

Da yake magana a lokacin da abin ya faru, Shugaban kungiyar matasa masu goyon bayan Buhari, Kabiru Lakwaya, wanda shi ne ya jagoranci wannan zanga zangar, yace sun yi wannanmaci ne domin nunawa Sowore cewar ba zai ci nasara ba a neman takarar Shugaban kasar da yake yi.

A cewarsa, sun yi watsi da Sowore ne sabida ajandarsa ta nuna kiyayya ga Shugaba Buhari da kuma yankin Arewacin Najeriya.

“A matsayinmu na matasa, bamu san wata gudunmawa da Sowore ya bayar domin cigaban kasarnan ba. Muna zaton wasu batagarin ‘yan siyasa ne suka dauke shi aiki, domin lalata mutunci da muhibbar Shugaba Buhari”

 

A lokacin da ya ziyarci Fadar Sarkin, Sowore yace, yazo ne domin ya gaida Sarki, saboda kudurinsa na ganin matasa sun samu ingantacciyar rayuwa.

LEAVE A REPLY