Lokacin da Shugabannin kungiiyar CAN suka kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar Gwamnati dake Aso Villa a kwanakin baya

Kungiyar magabatan kiristoci ta NCEF ta zargi kungiyar kiristoci ta CAN da yin almundahana da babakere akan kudaden da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na Naira miliyan 40 domin jin kai ga kungiyar kiristocin a yayin wata ziyara da suka kaiwa Shugaban kasa a fadarsa dake Aso Villa.

Kungiyar t magabatan kiristoci ta zargi CAN da yin boye boye akan wasu motoci da aka saya domin aikin kungiyar, da suka kira tsabar cuwa cuwa ce da rashin gaskiya da almundahana da babkere.

A wata wasika da kungiyar magabatan kiristoci ta NCEF ta rubutawa kungiyar CAN wadda Solomon Asemota, SAN ya sanyawa hannu, takardar ta zargi CAN da tsabar son kai da sakacin gudanar da aiki yadda ya dace.

Solomon Asemota ya bayyana cewar ya rubuta wasikar ne a madadin janar Joshua Dogonyaro mai ritaya da Zamani Lekwot da Janar Theophilus Yakubu Danjuma da Elder Matthew Owojaiye da Justice Kalajine Anigbogu (ret.) da Elder Shyngle Wigwe da Dr. Chukwuemeka Ezeife da kuma Pastor Bosun Emmanuel.

LEAVE A REPLY