Tsohon mataimakin Shugaban kasaa Atiku Abubakar tare da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, kuma jagoran kungiyara Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Asabar ya kaucewa halartar babban taron jam’iyyar APC na kasa da ya gudanaa babban birnin tarayya Abuja, inda ya ziyarci tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.

Wata majiya ta tabbatarwa da DAILY NIGERIAN wannan ziyarar da Kwankwason ya kaiwa Atiku, inda ta kara da cewar mutanan guda biyu kuma sun yi wata tattaunawa cikin sirri tsakaninssu a gidan tsohon mataimakin Shugaban kasa, taron da suka yi shi da misalin karfe 8:30 na dare.

LEAVE A REPLY