Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban jam’iyyar National Unity Party NUP na kasa, Cif Perry Opara ya bayyana cewa ba ya raba daya biyu in har tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019, to fa babu abinda zai hana ya baiwa shugaba mai ci, Muhammadu Buhari ruwa.

Opara ya bayyana haka ne ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ke cewa, “Kayar da Shugaba Muhammadu buhari zai yi matukar wahala a shekarar 2019, sai in fa Kwankwaso ne ya kara da Buharin.”

Opara ya yi kira ga Kwankwaso da ya zo ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar NUP, domin kuwa ‘yan Nijeriya na bukatar sabon shugabanci.

Ina bawa Kwankwaso tabbacin cewa in har ya tsayar da shawarar tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam’iyyar NUP kuma ya zabi mataimakinsa daga yankin kudancin Nijeriya wanda ya kamata ya zama matashi, natsattse kuma dan addinin Kirista mai riko da addini, to fa babu abinda zai hana Sanatan lashe zaben 2019.

Ko a ranar Larabar makon da ya gabata ma dai sai da wasu jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya suka halarci wani taro da jam’iyyar ta gabatar a Abuja.

LEAVE A REPLY