Masu yiwa kasa hidima

Daga Hassan Y.A. Malik

Kudirin dokar da za ta sahalewa mata masu bautar kasa sanya fatari a maimakon wandon da suke sakawa bisa al’ada ya gaza tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattijan Nijeriya.

Kudirin ya gamu da tasgaru ne saboda taba wancan bangaren dokar bautar kasa da ya dolanta amfani da khaki riga da wando ga mace da namiji, zai jawo taba ko kuma gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya kacokan dinsa.

A yayin da ya ke yin karin haske akan batun,  sanata daga jihar Taraba, Emmanuel Bwacha, ya bayyana cewa kudirin ya samo asali ne daga kokarin sassauta tsaurin da hukumar bautar kasa ke da shi na sai lalle mace ta sanya wando.

A cewar Bwacha, da a ce kudirin ya samu wucewa, da mata wadanda akidar addini da al’adunsa basu yarda da sanya wando ba, za su samu zabin saka wando ko fatari a wadannan makonni da ake yi a sansani ‘yan masu bautar kasar.

Sai dai kuma mataimakin shugaban majalisar dattijan, Sanata Ekweremadu ya bayyana cewa duk da muhimmacin kudirin sakamakon rahotanni da ke zuwa nan da can na cewa wasu mata na hakura da bautar kasa saboda basa so su saba wa koyarwar addininsu, amma babu yadda dokar za ta samu shiga ba tare da an gabatar da sauya a kundin mulkin kasa ba, kuma gabatar da canji akan kundin mulkinkasa na bukatar gudunmawa daga majalisun jihohi da na tarayya.

LEAVE A REPLY