Kanar Sambo Dasuki mai ritaya

Kotun koli a babban birnin tarayya Abuja, ta bayar da umarnin a cigaba da tsare tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Kanar Sambo dasuki me ritaya a gidan kaso har zuwa ranar 25 ga watan janairun 2018.

Kanar Sambo Dasuki, tsohon soja mai mukamin kanar, ya garzaya kotun koli ne yana kalubalantar cigaba da tsare shi da gwamnatin tarayya take yi, dan haka ne, ya nemi babbar kotun da ta tursasawa gwamnati sakinsa.

Sai dai, Kanar Dasuki yayi fatan babbar kotun zata umarci Gwamnatin tarayya da ta mutunta umarnin kotun daukaka kara dake Abuja da ta yi umarnin a sake shi,da kuma babbar kotun ECOWAS da itama ta bayar da umarnin a saki Sambo Dasukin.

LEAVE A REPLY