Maimuna Aliyu

Mai Shari’ah Mairo Nasir ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin Maimuna Aliyu, tsohuwar Darakta Gudanarwa ta Bankin bayar da Lamuni na Aso. Wadda aka zarga da yin zambar kudin da ya kai miliyan 57.

Maimuna Aliyu, itace mahaifiyar Maryam Sanda, wadda ta kashe mijinta kwanakin baya, Bilyaminu Bello a ranar 19 ga watan Nuwamban 2017.

Mai Shari’ar ta bayar da Maimuna Aliy beli, bayan da lauyen da yake kareta Jeo-Kyari Gadzama SAN, ya nemi a bayar da belinta.

Kotun ta bayar da belin nata, bisa sharadin dole mutum biyu su tsaya mata, kuma mutanan su kasance suna harabar kotun,kuma dole su yi rantsuwa kan zasu tsaya mata

Mai Shari’ar kuma, ta dage sauraren karar zuwa 12 ga watan Maris domin cigaba da sauraren karar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar hukumar ICPC a ranar 27 ga watan Nuwamban 2017, ta gabatar da wasu tuhume tuhume guda uku, wadda ta gabatar da su gaban kotun inda ake tuhumar Maimuna ALiyu da zambar kudade.

Haka kuma, Gadzama ya roki kotun domin dukkan takardun sharudan da ake bukata domin bayar da belin an cika su,kuma an gabatarwa da kotun su.

Sannan ya bukaci kotun da ta kalli wadda yake karewa a matsayin mai gaskiya kamar yadda sashi na 36 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.

NAN

LEAVE A REPLY