Aishah Ahmad

Daga Abba Wada Gwale

A ranar Alhamis ɗin yau ne fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ta turawa Majalisar Dattawa sunan Aishah Ahmad don su tabbatar da ita a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa, wato CBN.

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Mista Femi Adesina ya fitar, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawan da ta gaggauta tabbatar da Aishah don ta maye gurbin Sarah Alade, wacce ta yi ritaya a watan Maris.

Aishah, wacce aka haifa a ranar 26 ga watan Octobar shekarar 1976, ta shafe shekaru ashirin tana aikin banki.

Ta yi aiki a wurare da dama, wadanda suka haɗa da bankin Stanbic IBTC da bankin Zenith da kuma bankin New York Mellon.

Har ila yau Aisha, wacce ’yar asalin jihar Neja ce, ita ce jagorar sashen harkokin asusun ɗaiɗaikun mutane (Consumer Banking) a bankin Diamond.

A lokacin tana bankin Stanbic IBTC ta rike sashen kula da asusun masu hannu da shuni.

Ta yi digirinta na farko a fannin bayanan da suka shafi kuɗi (Accounting) a jami’ar Abuja, sannan ta yi digirinta na biyu a fannin sha’anin kuɗi a makarantar Cranfield School of Management ta ƙasar Birtaniya.

Aisha na auren birgediya janar mai ritaya Abdallah Ahmad, kuma suna da ’ya’ya biyu.

LEAVE A REPLY