Labari ne marar dadi da ya fara fitowa daga Tekun Meditereniya a farkon wannan shekara ga ‘yan Najeriya. Da yawan matasa masu hankoron zuwa kasashenTurai ta kowace irin hanya kan kare cikin mummunan yanayin marar misaltuwa.

Daruruwan matsa da ke yunkurin keta tekun Meditereniya domin zuwa kasar Italiya daga Afaurka, kan fada cikin mawuyacin halin da yake kaiwa zuwa ga salwantar da rayuwarsu. Ko a wannan lokacin ma irin hakan ce ta faru, domin wani jirgi da aka makare shi da masu keta teku zuwa Turai, sun gamu da ajalinsu a yayin da jirgin da suke ciki ya nitse.

Jirgin wanda ya tashi daga garin Azzawiyah da kuma Al Khums a kasar Libya ya nitse a teku da inda kimanin mutane 200 suka rasa rayukansu daga kasashen Afurka da dama, ciki kuwa har da Najeriya.

“Mafiya yawancin wadan da suka tsira sun ce, sun fito ne daga kasashen najeriya da Senegal da Mali sai kuma kalilan da suka fitodaga yankin Asiya mai nisa. Inji jami’ar kula da ‘yan gudun hijira mai aiki a Libiya Madan Petre Christian.

Zamu kawo muku cikakken bayanin an jima.

LEAVE A REPLY