Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar bagudu

Gwamna jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewar a jiharsa, babu wanda za’a daka aiki a harkarlafiya, sabida karancin daliban da suka karanci harkar lafiya ‘yan asalin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen mako, a yayin wani taron ganawa na kungiyar likitoci Musulmi.

A jihar Kebbi muna da bukatar ma’aikatan jinya da likitoci da sauransu, amma mun rasa wadan da suka yi karatu a fanni domin mu dauke su aiki, Inji Gwamna Bagudu! Gwamna ya kara da cewar, asibitocin jihar cike suke da bukatar ma’aikatan lafiya domin kula da lafiyar al’ummar jihar, amma shiru babu wanda suka yi karatu a sashen domin a dauke su aiki.

A dan haka Gwamnan yayi kira ga Sarakuna da malaman addini da kungiyoyi, das u yi kira ga al’ummar jihar das u rungumi karatu a sashin lafiya domin su zo su kula da al’ummar jihar.

Sannan Gwamnan ya bukaci kungiyar likitoci da ssu taimakawa jihar kebbi domin zaburar da mutane kan yin karatu a sashin lafiya.

Yaya kuke kallon wannan kalubale ga mutanen jihar Kebbi?

LEAVE A REPLY