‘Yan ata’adda sun sake farwa kauyukan Birnin Gwari guda hudu a yankin Kakangi dake jihar Kaduna.

Dan majalisa mai wakiltar yankin Birnin-Gwari da Giwa a majalisar wakilan Najeriya, Hassan Shekarau, ya taba gabatar da kuduri gaban zauren majalisar wakilai inda yake kiran da Gwamnati ta dauki matakan gaggawa a yankin nasa kan sha’anin tsaro.

Kwana guda bayan dan majalisar ya gabatar da wannan kuduri gaban zauren majalisar wakilai ta tarayya, ‘yan ta’addan ssuka farwa mazabarsda dake kakangi inda suka kashe mutane da dama a yankin.

Kauyukan da wadannan hare hare suka rutsa da su su ne Mashigi da Dakwaro da Sabon Gida da kuma Dakwaro.

Wani dan kungiyar ‘yan sintiri a yankin mai suna Malam Umar ya bayyana cewar ya zuwa yanzu sun sami gawarwakin mutane goma, yayin da saura suke warwatse a cikin daji, kuma ana kkarin kwaso su.

Haka kuma, ‘yan ta’addar sun bankawa gidajen jama’a wuta, tare da kunnawa rambunan ajiye hatsi wuta.

 

LEAVE A REPLY