Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai

A kalla mutane 40 ne ake kyautata zaton sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu mugayen raununka, a lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka yiwa garin Janruwa dake gundumar Maganda tsinke a yankin karamar hukumar Birnin-Gwari dake jihar Kaduna a ranar Asabar.

Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewar galibin wadan da wannan al’amari ya rutsa da su, mutane ne da suke aikin hako ma’adanai.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, maharan sun yiwa yankin kawanya da misalin karfe 12:45 na rana, inda suka fara harbin kan me uwa da wabi.

“A wani yanayi na nuna rashin Imani, maharan sun bankawa mutanan da suka mutu wuta, ta yadda ba za’a iya gane gawarwakin su ba” A cewar wata majiyar jami’an tsaron da ta nemi a sakaya sunanta.

Bayanai sun tabbatar da cewar, an ajiye gawarwakin mutanan da suka mutu a asibitin Jibril-Maigwari dake cikin garin Birnin-Gwari, yayin da har yanzuba a iya dauko wasu gawarwakin ba daga inda aka kashe su.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, akalla mutane 13 da suka samu harbin bindiga, yanzu haka suna karbar magani da samun kulawa a asibiti, yayin da wasu uku da suka samu munanan raunuka aka kaisu babban asibiti dake cikin jihar Kaduna.

“Adadin mutanan da aka kashe yana iya karuwa, yayin da jami’an tsaro da wasu mutane ‘yan sa kai suke cigaba da laluben mutanen da aka kashe a cikin dajin dake kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtuwa” A cewar Jibrin Alkali.

“Babu wanda zai iya cewa ga manufar wadannan maharan, amma sai dai wata majiya tace, mutanan suna daukar fansa ne a saboda kisan jagoransu da wasu mutanan yankin suka yi”

Wakilinmu ya gan cewar, hanyar da ta sadar da Birnin-Gwari zuwa Kaduna da kuma kauyukan dake da makwabtaka da wajen, sun yi tsit baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye.

“Mun kasance tamkar wadan da aka yi garkuwa da mu, a saboda haka muke neman agajin gaggawa daga Gwamnatin tarayya da kuma ta jihar kaduna” A cewar Alkali.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu, bai maido da amsar dukkan tambayoyin da aka aika masa ba ta wayarsa ta salula”

Sai dai kuma, Samuel Aruwan, mai magana da yawun Gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewar, Gwamnatin jihar Kaduna na karbar rahoton abubuwan da suka faru a yankinn na Birnin-Gwari, zata bayarda sanarwa daga zarar ta gama tattara bayanai kan abinda ya faru.

 

LEAVE A REPLY