Wasu mahara sun kashe akalla mutane 30 a kauyen Kabaro da Danmani a yankin karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Wani shaidun gani da ido, mai suna Shuaibu Kabaro, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a yankin karamar hukumar Maru, yace maharan sun kaiwa kauyukan biyu hari, an kuma sanar da jami’an tsaro nan take.

Yace an kama mutane uku daga cikin maharan, an kuma hannanta su ga jami’an tsaro domin daukar matakan da suka dace.

Malam Shuaibu yace, sun zo da mutane da yawan gaske domin yiwa kauyukan tsinke, inda suka kashe akalla mutane 30 a garin.

Shugaban karamar hukumar Maru, Salisu Dangulbi and da kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu duk sun tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

Acewarsu, mafiya yawan mutanen kauyen sun gudu daga gidajensusaboda tsoro sake aukuwar irin wadannan hare hare anan gaba da ka aiya aukuwa.

Amma muna ganin sakamakon kasancewar jami’an tsaro a yankunan da abin ya auku, mutane sun fara nutsuwatare da dawowa cikin hayyacinsu, suna komawa gidajensu.

Malam Shehu, ya kara da cewar, an tura karin jami’an tsaro da sojoji zuwa yankin da abin domin dawo da nutsuwa a yankin.

Sai dai kuma, jami’an tsaro sunce adadin mutanan da aka kashe na iya karuwa, domin har yanzu jami’an tsaro suna sake bibiyar alkaluman da mutanan da suka mutu..

NAN

LEAVE A REPLY