Jami’an ‘yan sanda a birnin Khartoum na kasar Sudan sun kaddamar da binciken kisan wani jami’in diflomasiyyar Najeriya, Habibu Almu a Sudan.

Habibu Almu wanda jami’in huumar kula da shige da fice ne na Najeriya, da aka tura shi Sudan dan gudanar da aikinsa a can, an same shi a mace jiya a gidansa dake Khartoum.

Binciken DAILY NIGERIAN ya nuna cewar Habibu Almu dan asalin jihar Katsina ne, an kashe shi jiya a Khartoum a gidansa bayan kwana uku da zuwansa Khartoum din daga Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Sudan Omar al-Mukhtar ya bayyana cewar an dabawa Almu wuka ne har ya mutu, inda ya bayyana cewar an yi masa kisan gilla ne, amma kafafen yada labarai musamman Al-Arabiya ta ruwaito kisan da cewar kisan ta’addanci ne aka yiwa jami’in.

Sai dai kuma, ‘yan sanda sun kashe mutane da dama da ake zargi kan kisan, saidai ana cigaba da gudanar da bincike dan gano wadan da suka kashe shi da kuma dalilin kisan.

LEAVE A REPLY