Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow

Mataimakiyar Shugaban kasar Gambiya, Fatoumata Tambajang, ta bayyana cewar kasar Gambiya zata iya rushewa matukar kwararru daga Najeriya suka janye hannayensu wajen ciyar da kasar gaba.

Madam Fatoumata Tambajang ta bayyana wannan kalami ne a wani taron karawa juna sani wanda kungiyar mata suka shirya karo na 62 a Gidan Najeriya, dake birnin New York a kasar Amurka a daren Alhamis.

Mataimakiyar Shugabar kasar, wadda ta samu wakilcin jakadan dindindin na kasar a majalisar dinkin duniya, Mamadou Tangara, ya bayyana cewar dole su jinjinawa Najeriya saoda irin goyon bayan da take basu.

Ta ce “Kasar Gambiya na alfahari da Najeriya, musamman irin goyon bayan da take samu daga Najeriyar. Idan har ‘yan Najeriya suka zare hannayensu daga tallafawa kasar to ba shakka Gambiya ta rushe baki daya”

“A takaice, idan kwararru daga Najeriya, musamman a sashin Shari’ah suka janye jikinsu, to sashin Shari’ah na kasar Gambiya ya rushe baki daya”

Kokari da hobbasar da Najeriya ta yi ne, ya sanya tsohon Shugaban kasar Yahya Jammeh barin gadon sarautar kasar a shekarar 2017, bayan ya yiwa maganarsa ta farko tutsu inda yace ba zai bayar da mulki ga Adama Barrow ba, bayan yayi alkawarin sauka.

‘Yan Najeriya sama da 30,000 ne suke zaune a kasar Gambiya, kuma sune ‘yan kasar waje mafiya yawa da suke zaune a kasar ta Gambiya.

Haka kuma, a cikin Bankunan kasar Gambiya guda 12, ‘yan Najeriya ne suke mallakar guda shida.

Dan Najeriya, Emmanuel Ayoola shi ne Cif Joji na kasar Gambiya a shekarar 1983 har zuwa 1992, haka kuma wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Fagbenle shima ya zama Cif Joji na kasar daga shekarar 2015 har zuwa 2017.

Mafiya yawancin kwararru a harkar Shari’ar kasar gambiya duk ‘yan Najeriya ne, hakan nan Lauyoyi da masana Shari’ah a kasar duk ‘yan Najeriya ne.

Akwai ‘yan Najeriya kwararru a fannin koyarwa da Likitanci da injiniya da sauransu da dama wadan da suke taimakawa kasar Gambiya.

Taron dai ya samu halartar mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed da kuma ministar harkokin mata ta Najeriya, Hajiya Jummai Aisha Alhassan.

LEAVE A REPLY