Shugaba Mugabe a lokacin da yake rattaba hannu kan takardar sauka daga Shugabancin kasar Zimbabwe

Kakakin Majalisar dokokin Zimbabwe Jacob Mudenda, a yau talata ya bayyana murabus din Shugaba Robert Mugabe daga Shugabancin kasar Zimbabwe da ya shafe shekaru 37 yana jan ragama, tun bayan da kasar ta samu mulkin kai daga kasar Burtaniya.

“Ni Robert Gabriel Mugabe, a bisa tanadin dokar kasarmu ta 96, ina mai mika takardar barin aiki na a matsayin Shugaban kasa, kuma wannan murabus zai fara aiki nan take” Kakakin Majalisar Dokokin kasar Zimbabwe Mista Jacob Mudenda, yake karanta takardar Murabus din Shugaba Mugabe.

LEAVE A REPLY