Rundunar sojan sama ta Najeriya ta rasa jirgin helikwafta mai lamba Mi-17 yayi wani mummunana hadari a lokacin da yake fuskantar abokan gaba na masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso gabas.

Lamarin dai ya auku ne a yau, 8 ga watan Janairu 2018, a dalilin muguwar illar da jirgin ya samu a sakamakon wannan hadari, a cewar kakakin rundunar sojan sama ta Najeriya, Olatokunbo Adesanya.

Sai dai bai bayyana ainihin inda jirgin yayi hadarin ba. “Sai dai babu asarar rai ko daya a sanadiyar wannan hadari”

“Babban hafsan sojan sama na Najeriya, Mashal Sadik Abubakar, ya bayar da umarnin a kafa kwamitin da zai binciki musabban faruwar wannan lamari”

 

LEAVE A REPLY