Kanu Nwankwo

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Nijeriya, Kanu Nwanko ya bayyana muradinsa na son tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar zabe ta 2019.

Tsohon dan wasan da ya yi shuhura a lokacin yana taka leda a kungiyoyin Arsenal, PSV da Inter Milan ya bayyana nasarar da George Weah ya yi na zama shugaban kasar Liberia ne ya kara masa kwarin gwiwar son ya tsaya takarar.

A wata hira da ya yi da mujallar yanar gizo ta Goal.com ya ce: “Dalilina na zuwa nan shi ne don tabbatarwa da kasata Nijeriya gobe mai kyau tare kuma da samawa ‘yan Nijeriya walwala.”

“Nijeriya a shekaru 18 din da suka gabata bata yi dace da matuka na gari ba, inda ta ci gaba da samun koma baya a kowane bangare na tattalin arziki da tafiyar da gwamnati.”

“Haka kuma ina so na fuskaci cin hanci da rashawa ta yadda zan tuge shi daga tushe. Wannan ko shakka babu zai dawo da kimar kasar a idon duniya.”

“In har ku ka kada min kuri’u na zama shugaban kasa, to, zan dawo da martabar aikin gwamnati ta hanyar baiwa wadanda suka dace da aikin dama don su bada gudunmawarsu.”

“Nasarar da George Weah ya samu manuniya ce da ke tabbatar min da cewa wannan buri nawa zai tabbata da goyon bayanku,” Kanu ya ce.

Kanu, mai shekaru 41, zai fito da nufin kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019.

LEAVE A REPLY