Gwamnatin jihar Taraba a Arewa maso gabashin Najeriya, na shirin baiwa matasa 1,000 horo na musamman akan yadda zasu dinga hana Fulani yin kiwo a yankunansu. Wani Bincike ne ya tabbatar da hakan.

Duk da cewar an ja hankalin Gwamnatin kan daukar irin wannan mataki, amma Gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu, ta cigaba da gudanar da shirin baiwa matasan horo na musamman domin hana Fulani kiwo a dukkan kananan hukumomin jihar.

Gwamnan jihar, Mista Darius Ishaku, ya fada tun farko cewar,babu wani fili domin Fulani suyi kiwo a jihar. bayan haka, Ishaku ya tabbatar da cewar dokar da jihar ta yi na hana Fulani yin kiwo a jihar zata fara aiki a watan Janairun 2018.

DAILY NIGERIAN ta fahimci cewar, idan har aka aiwatar da aiki da wannan doka, to dukkan wanda yake da dabbobi tilas ne ya tanadi filin da zasu yi kiwo, amma ba yawo ba kamar yadda aka saba.

Wani jiyau ya tabbatar mana cewar, Gwamnatin zata yi amfani da wasu tsaffin sojoji domin baiwa matasan Horon a sansanin masu yiwa kasa hidima dake jihar, domin su yi aiki a dukkanin mazabun kananan hukumomin jihar 16.

Majiyar ta kuma tabbatar mana cewar, akwai karin mutane 680 da gwamnatin zata dauka domin basu irin wannan horo da take shirin yi.

“Muna da mazabu 168 a jihar Taraba, a sabida haka, kowace mazaba an shiri samun mutum 10 da za’a basu wannan horo na hana Fulani kiwo a yankunan su” A cewar Gwamnatin taraba.

Sai dai kuma, kungiyar Fulani ta Miyatti Allah, ta yi tir da wannan yunkuri na Gwamnatin Taraba, a cewar wannan abu ba komai bane, illa yunkurin sanya mutane su dinga kaiwa Fulani hari a yankunansu.

Shugaban gamayyar kungiyar Fulanin, Sahabi Tukur, yace aiwatar da wannan doka da gwamnatin ke shirin yi na da matukar hadarin gaske, domin a cewarsa, sam yin irin wannan doka bata dace ba ko kadan.

TSahabi Tukur, yace manufar Gwamnati itace kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu, ba tare da la’aari da jinsi ko kabila ko addini ba.

“Aiwatar da wanna doka cikin gaggawa ba karamar illa zata yiwa wannan gwamnatin ba, domin yin hakan sam bai dace ba a irin wannan hali da ake ciki, domin za’a baiwa matasan dama ne kawai su dinga kaiwa fulani hari suna kashe su”

Sai dai kuma, a lokacin da yake mayar da martani kan wannan batu, mai taimakawa gwamnan jihar akan kafafen yada labarai, Bala Abu, ya kalubalanci kungiyar Fulani da su zo da hujjar inda Gwamnanatin jihar ta bayar da wancan umarni na horas da matasa.

“Muna sane da yunkurinsu na yin kafar ungulu ga kokarin Gwamnan jihar Taraba na samar da zaman lafiya a jihar ta hanyar aiwatar da dikar da zata hana Fulani makiyaya shiga yankunan mutane domin yin kiwo”

 

LEAVE A REPLY