Minista harkokin zirga zirgar jiragen sama na kasa Hadi Sirika ya tabbatar da cewar kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Najeriya zai fara jigilar diban mutane nan da karshen shekarar nan.

Minsitan wanda tsohom matukin jirgin sama ne, ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake bayyana takardun amincewar da kamfanin ya samu domin fara yin zirga zirgar jiragen sama da hukumae dake kula da yin hakan ta sahale masa.

The Outline Business Case Certificate issued by the ICRC for the National Carrier

Sirika ya kara da cewar bayyana wannan satikifek na fara wannan jigila da kamfanin zai yi, ya nuna irin yadda aka himmatu wajen ganin an samar da wannan katafaren aiki wanda zai taimakawa al’ummar kasarnan akan harkokin sufurin jiragen sama.

Ya cigaba da cewar Gwamnati ba zata yiwa kamfanin katsalandan a harkokin gudanarwasa ba, za’a bashi dukkan wata dama domin yin aiki kafada da kafada da sauran kamfanin jiragen sama takwarorinsa na kasashen duniya.

A cewarsa, idan kamfanin jirgin saman Najeriya ya fara aiki zai doke dukkan wasu kamfanunnukan jiragen sama dake nahiyar Afurka wajen sauki da kuma kyautatawa abokan hulda.

 

LEAVE A REPLY