Zanen taswirar Najeriya,inda take nuna zanen karamar taswirar jihar Kaduna da aka sanyawa jan launi

Kimanin mako guda kenan da aka kai wani hari da yayi sanadiyar mutuwar mutane 40 a jihar Kaduna, inda aka kashe wasu masu hakar zinare da azurfa a kauyen Janruwa, a yankin karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna.

‘Yan ta’addar sun kuma yunkurowa inda suka kashe mutane 27 a kauyen dake makwabtaka da inda aka yi kisan mutane 40 a makon da ya gabata.

A ranar 3 ga watan Mayun nan, Sufeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Kpatom Idris da ya ziyarci yankin birnin Gwari ya bayar da umarnin a tura karin ‘yan sanda 200 zuwa yankin na Birnin-Gwari domin dirarwa mahara da masu garkuwa da mutane.

Amma sai dai wani shaida ya tabbatarwa da DAILY NIGERIAN cewar duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, maharan sun cigaba da kai munanan hare hare a yankin tun kusan misalin karfe 2:30 na rana a jiya Asabar, inda suka kashe mutane 27 mafi yawansu mata da yara a kauyen Gwaska.

“Yan ta’addar da ake kyautata zaton sun fito ne daga jihar Zamfara, sun yiwa kauyen na Gwaska tsinke, har zuwa kauyen Kuiga inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi” A cewar wani dankato da gora a yankin, Sule Kassim.

“Haka kuma, maharan sun cinnawakauyen wuta, inda suka kone a kalla gidajen kauyen 3000 kurmus”

Wani da ya samu tsira da ransa, ya bayyana cewar, mafiya yawan wadan da aka kashe, ‘yan sa kai ne wadan da suka bayar da rayuwarsu domin kare kauyen da al’ummar dake ciki.

Wani mamba a cikin ‘yan sintiri na garin Birnin-Gwari wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace, mutanen da aka kashe yawansu yafi 27, yace zasu fadi adadin mutanan da suka mutu yayin da suka gama debo gawarwakin da suke warwatse a cikin kauyen.

“Muna kara yin kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin kare al’ummarda suke shugabanta, daga hare haren wadannan makiya miyagu azzalumai”

Yankin karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, ya sha fama da hare haren ‘yan ta’adda inda aka kashe mutane da daman gaske.

LEAVE A REPLY