Tsohon Shugaban riko na jam'iyyar PDP Sanata Ahmad Muhammad Makarfi

A ranar Asabar Jam’iyyar PDP ta bayyana rushe Shugabancin Kwamatin riƙon jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnana jihar Kaduna Sanata Ahmed Myhammad Makaarfi. Rushe Shugabancin dai ya biyo bayan cikarwa’adin da aka baiwa Makarfi domin jagorantar jam’iyyar har zuwa ga yau da ake sake sabon zabe.

Jam’iyyar PDP na zabe sabonShugaban jam’iyyar ranar Asabar a birnin tarayya dake Abuja. Zaben wanda ake sa ran za’a zabi sabbin Shugabannin da zasu ja ragamar jam’iyyar har zuwa nan da Shekara hudu.

Bayana haka, sabon Shugabancin Jam’iyyar shi ne zai zabi wanda zai yiwa jam’iyyar takarar Shugaban ƙasa a zaben shekarar 2019 dake tafe. Dan haka ne, masu nazarin siyasa ke cewar wannan zabe da PDP take yi yana da matukar muhimmanci a gareta.

Tuni dai wasu da suke takarar Shugabancin jam’iyyar suka janye daga neman Shugabancin, irinsu Bode George da Tunde Adeniran da kuma Remond Dokpesi, wanda suka ce sun fice daga takarar Shugabancin jam’iyyar.

Yayinda ake ganin Uche Secondus wanda galibin Gwamnonin jam’iyyar suke goyawa baya shi ne zai samun nasarar zama Shugaban jam’iyyar na gaba.

LEAVE A REPLY