Babban zaben jam'iyyar PDP na kasa

Babban filin taro na Eagle sukwaya yau ya cika makil da magoya bayan jam’iyyar PDP wanda suka taru domin sake zaben sabbin Shugabannin jam’iyyar na kasa. Ana ta kade kade da bushe bushe da wakokin tsuma zukata na jam’iyyar a harabar filin da ake gudanar zaben.

Rahotanni dai sun ce, fiye da mutane 2000 ne aka tantance wadan da zasu zabi sabbin Shugabannin jam’iyyar a babban taronta na kasa da take gudanarwa. Daman kuma a yau, din, jam’iyyar ta bayar da sanarwar rushe kwamitin riko na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi.

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonthan da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da ya koma jam’iyyar ba da jimawa, da Tsaffin Gwamnonin jam’iyyar da masu ci da kuma tsaffin ministoci duk sun hallara domin shaida zaben sabbin Shugabannin.

Tuni dai wasu daga cikin masu neman Shugabancin jam’iyyar suka bayyana janyewarsu, kamar su Bode George da Jimi Agbaje da Gbenga Daneil duk sun bayyana janyewa daga zaben. Wadan da suke kan gaba wajen neman Shugabancin dai sun hada da Uche Secondus wanda ake ganin Gwamnonin jam’iyyar na mara masa baya da kuma Mista Tunde Adeniran da Shugaban gidan talabijin na AIT Reymond Dokpesi.

Nan gaba ne dai ake sa ran za’a bayyana sakamakon zaben wanda ya lashe zaben Shugabancin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY