Jami’an tsaron farin kaya na DSS sun tare kofar shiga harabar majalisar dattawa ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja. A yayin da Shugaban majalisar Bukola Saraki ya yi kiran zaman gaggawa.

An dai tunanin cewar ana son ayi amfani da wannan zaman na yau ne domin tsige Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ko ta wanne hali.

Su dai jami’an tsaron sun hanawa Sanatocin jam’iyyar PDP shiga harabar majalisar, har sai da SAnatocin suka yi amfani da karfi suka shiga harabar majalisar. Amma dai majalisar bata samu ta zauna kamar yadda aka shirya ba sakamakon dambarwar daaka yi tsakanin jami’an tsaro da Sanatoci masu nuna goyon baya ga Shugaban majalisa Bukola Saraki.

 

LEAVE A REPLY