Hassan Y.A. Malik

Kwanaki 51 bayan da Fulani makiyaya suka afkawa garuruwan Guma da Logo a jihar Binuwe, inda suka kashe mutane 73, yawancin su mata da kananan yara, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da cakfe mutumin da ya jagoranci harin tare da wasu mutane 3.

Haka zalika mutane hudun na da alaka da kisan wani sufeton ‘yan sanda, Solomon Dalung, da wasu jami’an ‘yan sanda kwanaki kadan bayan harin wancan harin na Binuwe.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan nasara ta biyo bayan sharudan da sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris ya bawa sashen rundunar na IRT.

An kama mutanen hudu tsakanin 16 da 19 ga watan nan a dajin Tunga da ke jihar Nasarawa dauke da muggan makamai da bindigogin AK47, kamar yadda rahotan jaridar Vanguard ya bayyana.

Mutanen sun hada da Alhaji Laggi mai shekaru 40, wanda shi ‘yan sanda suka kira jagoran harin, sai Mallam Mumini Abdullahi, mai shekaru 34, Muhammed Adamu mai shekaru 30 da Ibrahim Sule mai shekaru 32.

‘Yan sanda na ci gaba da tsefe dajinan Binuwe, Taraba da Nasarawa a yunkurin su na kama sauran wadanda ke da hannu a lamarin.

LEAVE A REPLY