Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, a ranar Juma’a, ta bayyana cewar, a zaben kananan hukumomin jihar Kano da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata an tafka kazamar cuwa cuwa, ta yadda aka ki yin amfani da takardun zaben da INEC ta baiwa hukumar zabe ta jihar Kano.

Tun da farko dai an zargi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da yin katsalandan wajen tafka muna muna a zaben kananan hukumomin, inda kuma aka yi zargin kananan yara da shekarunsu basu kai zabe ba an basu dama sun kada kuri’a zaben.

Bayan da aka yiwa wadancan zarge zargen a zaben kananan hukumomin na jihar Kano, hukumar zabe ta kasa, INEC, ta kafa wani kwamiti karkashin wani kwamishina a hukumar Abubakar Nahuche domin bincika zarge zargen da aka yi a zabn.

Bayan da kwamitin yayi aikinsa, ya mikawa Shugaban hukumar zaben ta kasa Farfesa Yakubu sakamakon binciken inda aka gano yadda aka yi almundahana a zaben da ya gabata.

LEAVE A REPLY