Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya bayyana aniyarsa ta yin takarar Shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2019. Shugaban majalisar dai ya bayyana cewar yana sharwari kan batun tsayawarsa takarar Shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar PDP idan ta bashi dama.

Saraki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Bloombarg. Ya ce “Ina da kwarin guiwar cin zabe idan har sabuwar jam’iyyata ta bani dama, domin zan samar da canji na gaskiya da ‘yan Najeriya ke muradi” A cewar Saraki.

Jam’iyyar PDP dai ta sanya watan Oktoba mai zuwa a matsayin lokacin da zata shirya tare da gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarar Shugaban kasa.

Saraki ya kara da cewar, a yanzu PDP ta dauki darasi kan faduwarta zaben 2015, kuma ba zata yi sake da wannan damar da ta samu ba.

 

 

LEAVE A REPLY