Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jihar Kano yayin da yake ganawa da kungiyoyin al'umma

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, yana martukar yadda wai PDP take son dawowa kan karagar Mulki a Najeriya, bayan duk irin muguwar barnar da ta aikatawa kasarnan wai har wani shirye shirye suke yi na sake dawowa kan karagar mulki a babban zaben 2019 da ke tafe.

Shugaba Buhari yana magana ne, a taron kungiyoyin al’umma da da aka gudanar a gidan Gwamnatin Kano, a bukuwan da ake yi na ziyararsa a birnin Kano ta yini biyu, wadda ta kare a ranar Alhamis. Shugaba Buhari yace ‘yan Najeriya ba zasu taba mancewa da mulkin shekaru 16 na jam’iyyar PDP ba.

Kamar yadda ya fada, cin hanci da rashawa bai sake samun gindin zama ba, sai a zamanin mulkin PDP a Najeriya. PDP sai da ta kusan tsiyata Najeriya, kuma ita ke da alhakin dukkan wannan balahira da batarnaka da ake yi ta cin hanci da rashawa a Najeriya. Dan haka babu abinda PDP ta yi illa muguwar barna a Najeriya.

Ya cigaba da cewar, tsarin Gwamnatin APC shi ne samar da canji, ta hanyar yakar fitinar Boko Haram, da yakarcin hanci da rashawa, da kuma samar da tsarin da tattalin arzikin Najeriya zai dawo cikin hayyacinsa. Dan haka wannan Gwamnatin ta APC tana samun nasarori sosai akan abinda suka sanya a gaba, inji Buhari.

Shugaba Buhari ya kara da cewar,” Amma yaki da cin hanci shi ne abinda yafi ci mana tuwo a kwarya. Dan haka tilas ne ‘yan Najeriya su fahimci bambancin tsarin Gwamnatin soja da kuma Gwamnatin Demokaradiyya. Tun zamanin da nayi Mulki cin hanci da rashawa yake yunkurin kashe kasarnan, ni kaina sai da na kare a gidin kaso a sakamakon yakin da na kuduri aniya da cin hanci.”

“A lokacin da nake shugaban kasa a mulkin soja, na kama kuma na tsare ‘yan siyasa da yawa, sabida a lokacin ina da kuruciya, amma mutumbiyu daga cikin wadan da muka kama, muka ga ashe su ba masu laifi bane, marigayi Bilyaminu Usman da kuma Malam Adamu Chiroma, su kadai ne bamu samu da laifi ba, a cikin mutanen da muka kakkama a wancan lokacin.”

“A wannan kasar ne fa muka samu wani babban alkali, makare da kudaden kasashen waje a gidansa, na miliyoyin kudi, da fasfo na musamman har kala hudu.  Irin wadannan mutanen fa sune suke daure mutane shekaru 20 sabida sunci hanci ko sun karbi rashawa, amma sai gashi mai dokar barci ya bige da gyangyadi.” Inji Buhari.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya tunawa mutane cewar,daga shekarar 1999 har zuwa 2014 Najeriya na fitar da gangar danyan mai Miliyan biyu da digo daya (2.1m) a kusan farashin da bai gaza dalar amurka 100 ba, yace wadannan makudan kudade duk sunyi batan dabo a karkashin mulkin PDP.

“Abin takaici, lokacin da muka karbi mulki farashin gangar danyan mai ya karye, inda ake sayar da kowace ganga akan dalar amurka 28, sai daga bisani ne ta daga zuwa 37 har ta kai 40. A dan haka naje Babban bankin kasa CBN domin a lokacin kowa yasan nawa ne Najeriya take samu daga danyan man da take kasuwancinsa, na tambayi nawa muke da shi a ajiye, aka shaida min cewar, babu komai, sai ma ciko da ya biyo gyartai.”

“Ban iya gamsu da bayanin ba, sabida ina tunanin kamar ba gaskiya bane. Aka ce min wai anyi amfani da kudaden wajen shigo da mai da kayan abinci, bayan kuma nasan a yankunan kudu maso yamma, da maso gabas da maso kudu, da kuma Arewa maso yamma da maso gabas da Arewa ta tsakiya duk muna iya samar da abincin da zamu ci, nace ba zai yuwu ba mu dinga siyan abincin kasar waje, wannan rayuwar karya ce.”

“A lokacin da muka bincika yadda ake shigo da tattacen mai, abin takaici, mun samu kazamar cuwa cuwa tsakanin masu shigo da man da kuma masu kasuwancinsa a gida Najeriya tare kuma da hadin bakin babban bankin kasa CBN. Samko a jikinsu basu damu da halin da ‘yan Najeriya zasu fada ba ta sanadiyar ci da guminsu da suke yi.”

Tare da irin wannan mugun alkaba’in da aka yi a Najeriya karkashin Gwamnatin PDP ta tsawon shekaru 16, wai suna shirye shiryen dawowa kan karagar mulki, ni kam ina cike da mamaki a gaskiya. Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma, yayi godiya ga al’ummar jihar Kano akan irin goyon baya da suke bashi, da kuma karrama shi da aka yi a yayin wannan ziyara da ya kawo, naga har da kananan yara sun fito sosai kawai dan su yi ido biyu da ni gaskiya ban yi tsammanin haka ba, “Na gode kwarai da gaske mutanen Kano” Inji Shugaba Buhari.

 

LEAVE A REPLY