Buba Galadima

Shugaban sabuwar jam’iyyar APC ta kasa wanda suka balle suka kafa sabon Shugabancin jam’iyyar karashin Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewar yanzu haka idan ya nemi ‘yan majalisa su fara shirin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wuri zasu yi hakan domin kuwa ‘yan bangarensa na sabuwar APC suke da rinjaye akan ‘yan tsohuwar APC.

Buba Galadima na yin wannan kalami ne domin maida martani ga tsagin APC karkashin jagorancin Adams Oshiomhole wanda suka caccaki sabuwar APC da Shugabancinta karkashin Buba Galadima.

Buba Galadima ya kuma kuduri aniyar cigaba da jajircewa kan Shugabancin jam’iyyar da yake yi. Inda ya bayyana zabensa da aka yi don ya jaoranci jam’iyyar a matsayin wani abu da ya dace domin ciyar da jam’iyyar gaba.

Ya kuma karada cewar yanzu haka ‘yan bangarensa na sabuwar APC su ne suke da rinjaye a majalisun dokokin tarayyar Najeriya bisa ga ‘yan APC kaarkashin Adams Oshiomhole, a saboda haka ya bayyana cewar da zai yi kira a tsige Shugaba Buhari da gudu zaa ai hakan.

LEAVE A REPLY