Shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Yakubu

Hukumarzabe ta kasa, INEC, a rnar talata ta saki jadawalin babban zaben kasa na shekarar 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a Abuja, inda yace, lokacin zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya zai kasnce a ranar 16 ga watan Fabrairu 2019; sannan zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi kuma zai kasance ranar 2 ga watan Maris 2019.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya tuna cewar tun a baya hukumar zaben ta kasa ta fitar da ranakun zaben 2019 tun a watan Maris din 2017.

Mista Yakubu, wanda shi ne Babban Baturen zabe na kasa yace, zaben fitar da Gwani wanda jam’iyyu zasu yi a matakin kasa da kuma jihohi zai kasance tsakanin 18 ga watan Agusta, 2018 zuwa 7 ga watan Oktoba, 2018.

Haka kuma, zaben fitar da Gwani da ya shafi babban birnin tarayya Abuja, an tsara zai kasance tsakanin ranakun 4 zuwa 27 ga watan Oktoba, 2018.

Baturen zaben na kasa ya kara da cewar, dukkan yakin neman zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya zai fara ne daga ranar 18 ga watan Nuwamba, 2018; sannan ya kare a ranar 14 ga watan Janairu, 2019. Sannan kuma, na Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi zai fara daga ranar 1 ga watan Disamba 2018, zuwa 28 ga watan Fabrairu 2019.

Haka kuma, hukumar zabe ta kasa, zata fara karbar takardun tsayawa takara daga hannun jam’iyyu a ranar 17 ga watan Agusta zuwa 24 ga watan Agusta, sannan kuma na babban birnin tarayya Abuja zai kasance tsakanin 3 ga Satumba zuwa 1 ga Satumba, 2018.

Baturen zaben na kasa ya cigaba da cewar, ranar karshe ta mayar da takardun cikewa domin shiga zabe da jam’iyyun siyasazasu mayar ita ce 3 ga watan Disamba, sannan kuma, na Shugaban kasa da ‘yan majalisun dokoki na kasa da na jihohi zai kasance 17 ga watan Disamba 2018.

Ya kara da cewar, Birnin tarayya Abuja za a mayar da takardun cikewa domin shiga zabe a ranar 3 ga watan Nuwamba zuwa 10, sannan kuma ranar ta karshe ta rufe karbar takardun ita ce 14 ga watan Disamba.

Hukumar zaben, a cewar Shugabanta Farfesa Yakubu, zata wallafa bayanai dan gane da ‘yan takarar Shugaban kasa da na majalisun dokokina tarayya a ranar 25 ga watan Oktoba, sannan na ‘yan takarar Gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2018.

Sannan kuma, hukumar zaben ta kasa ta sanya ranar 17 ga watan Nuwamba a matsayin rana ta karshe da za’a iya musanya dan takara tun daga Sugaban kasa har zuwa kana ‘yan majalisu na tarayya ko janye sunayensu. Sannan ranar 1 ga watan Disaba domin musanya sunan dan takarar Gwamna ko na dan majalisar dokoki na jiha.

Farfesa Yakubu, ya cigaba da cewar, INEC a ranar 2 ga watan Janairu, 2019 zata wallafa bayanai na karshe gama da dukkan ‘yan takararkaru dabandaban, sannan kuma a ranar 7 ga watan Janairu, 2019 ta wallafa dukkan bayanai game da masu kada kuri’a.

Shugaban hukumar ya kara da cewar, hukumar na sa ran karbar sunayen wakilan jam’iyyu a wajen zabe a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2019.

Haka kuma, ya bayyana cewar akwai mazabu 1,558 wanda a cikinsu ne ake gabatar da zaben Shugaban kasa, da kuma  zaben  Gwamnoni 29 wadan da za’a gudanar a zaben 2019.

Mista Yakubu ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewar hukumar zabe ta kasa zata yi dukkan kokarinta wajen ganin ta baiwa mara da kunya wajen cika alkawari kamar yadda ta tsara.

Ya cigaba da cewa, hukumar zabe ta kasa na bukatar goyon bayan ‘yan Najeriya da hadin kansu da kuma dukkan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar wannan zabe. Sannan kuma, ya tabbatar da cewar, hukumar zata yi biyayya ga dukkan dokokin da suka kafa hukumar wajen cin nasarar ayyukanta.

Ya sha alwashin cewar, hukumar zabe ta kasa, ba zata bar baya da kura ba a dukkan irin abubuwan da ta shirya gudanarwa domin gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali da gaskiya.

“A yau, sauran kwanaki 402 a bude rumfunan zabe a dukkan fadin Najeriya a ranar 16 ga watan fabrairu da misalin karfe 8 na safiyar ranar wannan Asabar”

“Kamar yadda jam’iyyu da kuma ‘yan takara suke neman goyon bayan masu zabe, hukumar zabe ta kasa na fatan, za’a gudanar da lamura cikin tsanaki da girmama juna”

Baturen zabe na kasa ya kara da cewar, hukumar zabe ta kasa zata bayyana irin adadin kudaden da za’a kashe a wannan zabe daga zarar ta kammala wani zama na musamman da zata yi a ranar Alhamis.

Ya kara da cewar, a ranar 13 ga Janairu da za’a gudanar da zaben cike gurbi na dan majalisar dattawa da aka tsara tun farko za’a yi a jihar Anambara tana nan ba a sauya ba.

Sannan kuma, ya bayyana cewar, fiye da kungiyoyi 100 suka nemi hukumar zabe ta kasa ta yi musu rejista a matsayin jam’iyyun Siyasa.

Sannan ya tabbatar da aniyar hukumarsa ta yiwa duk wata kungiya da ta cika ka’ida rejistar zama jam’iyyar siyasa, kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada.

NAN

LEAVE A REPLY