Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS, sunci nasarar cafke kasurgumin dan daban nan mai sace mutane yayi garkuwa da su domin neman kudin fansa a jihohin Filato da Binuwai da Nassarawa da kuma Taraba.

A wata sanarwa da hukumar ta DSS ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Tony Opuiyo, ya bayyana cewar jami’an binciken musamman ne suka ci lagon rikakken dan daban, John Abbey inda suka yi masa kofar rago tare da mai tuka shi a mota wanda aka fi sani da Dan-Wase a garin Wukari ta jihar Taraba.

A cewar Mista Opuiyo, shi wannan dan daba Mista Abbey ya jima cikin jerin mutanan da hukumar DSS ke nema ruwa a jallo, tun kusan shekaru goma da suka wuce, sabida yadda yake kasuwanci shigo da makamai ta barauniyar hanya.

Ya kara da cewar, shi wannan dan ta’adda Abbey, ya jima yana yiwa barayi da ‘yan daba hidima a jihohin Bayelsa da Ebonyi da Ribas da Imo da Anambra da Filato da Nassarawa da Binuwai da kuma Taraba, mutane irinsu Terwase Akwaza wanda shima wani dan ta’adda ne, duk shi Abbey ke samar musu da makamai.

onah Abbey and his driver Dan-Wase

“Binciken baya bayan nan sun nuna cewar Abbey yana shigar da makamai masu hadari daga garin Kunduga na jihar Borno zuwa jihar Taraba ta hanyar amfani da mai tukashi a mota”

“Shi dai wanna rikakken dan ta’adda ance yana samun makamai ne daga jamhuriyar Kamaru da kuma yankin Arewa maso gabas mai fama da rikici a Najeriya”

“Haka kuma a wani samame da jami’an hukumar DSS suka kai a ranar 15 ga watan maris din nan 2018, da misalin karfe 0500, a otal din Chiwarna dake Unguwar Rogo kan titi Bauchi a Jos ta Arewa an ci nasarar kama wani mugum dan ta’adda mai suna Lawal Ibrahim wanda aka fi sani da Alhaji Awalu.

“A yayin wannan samame an kuma kama wasu na hannun daman dan ta’addar da suka hada da wani mai suna Ado Saleh da kuma Bayero Adamu. Wadannan sune ke da hannu wajen kisan jami’an tsaro da dama a jihar, haka kuma, Daanan Balgnan a ranar 30 ga watan Disamba ya sace tare da garkame wasu jami’an tsaro a jihohin Nassarawa da Kaduna da kuma Bauchi”

“A yayin da aka ci nasarar kama wadannan gaggan miyagun mutane, an samu zunzurutun kudi Naira miliyan daya da rabi a hannunsu”

“Kudin suna daga cikin wasu kudin fansa Naira miliyan biyu da suka karba daga hannun wani mai suna Ayuba Gamale jami’in hukumar ITF wanda suka sace biyu daga cikin iyalansa suka kuma sake su ranar 14 ga watanMaris din nan bayan sun karbi kudin fansar. Haka kuma, jami’an tsaro na DSS na cigaba da farautar sauran ‘yan ta’addar”

Items recovered from the kidnappers/criminals

 

Daga cikin abinda aka samu a wajen rikakken dan ta’adda Abbey ahr da miyagun makamai da albarusai, da kanana da manyan bindigogi kirar gargajiya da wukake da sauransu.

 

LEAVE A REPLY