Mutanan da ake tantancewa a fatima Hall kenan

Hukumar tattara kudaden haraji ta kasa FIRS, tana gudanar da tantance daukar ma’aikata cikin sirri a jihohin Kano da legas da Fatakwal.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu lekawa inda ake yin wannan tantance ma’aikatan da za’a dauka cikin sirri a jihar kano, inda aka kira mutane kimanin 769 ta hanyar aika musu da sakon tes, na kiransu da su zo a tantance su domin daukansu aiki a hukumar.

A hotal din Grand Central Hotel dake kano ake yin aikin tantancewar a wani daki mai suna Fatima Hall. Idan ba’a manta ba, a watan nuwamban shekarar da ta gabata, shugaban hukumar babatunde Fawler ya sanar da cewar fiye da mutum 700,000 suka aiko da takardunsu domin neman a dauke su aiki a hukumar.

haka nan kuma, a asirce a watan Yunin shekarar da ta gabata, hukumar ta dauki ma’aikata kimanin 349 ba tare da anbi ka’idar daukar ma’aikata da dokar kasa ta tanadar ba. An kalubalanci hukumar a wannan lokacin kan daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba a lokacin, sai gashi yanzu ma an sake kwata irin abinda ya faru a baya.

Wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA da ya samu zuwa dakin da ake gudanar da wannan tantancewar, ya samu an kasa mutanan da za’a tantance gida gida, domin yi musu tambayoyi.

Me ye ra’ayinku kan wannan batu?

LEAVE A REPLY