Ginin gidan matar tsohon Shugaban kasa Patience Jonathan da aka rushe jiya a Abuja

Wani katafaren gini mallakar matar tsohon Shugaban kasa Dame Patience Jonathan ya gamu da fushin hukumar raya birnin tarayya Abuja a ranar talata, inda aka rushe shi har kasa ba tare da wani bata lokaci ba.

Ginin wanda yake a rukunin gidaje na Mabushi akan titin Shehu YarAduda a unguwar Kado-Life-Camp a birnin tarayya Abuja.

Mista Emmanuel Anene, wani lauya mai zaman kasan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewar, batun wannan gini abu ne da yake gaban wata kotun tarayya dake Legas da Abuja.

“Wani lokaci can baya, wasu mutane daaga hukumar raya birnin tarayya sun zo wajen da filin yake, inda suka ce, an fara yin ginin ba tare da izni daga hukumar ba”

“Mun je har ofishinsu muka same su, mun kuma nuna musu takardun da suke tabbatar da fara yin ginin da iznin hukuma, kuma sun yadda da sahihancin takardun. Mun zaton batun ya wuce tun a wancan lokacin”

“”Kuma daman tun wani lokaci sun kai kara kotu, suna kiran sai an mallakawa Gwamnati wannan ginin, wanda a Legas kotu bata basa damar karbewa ba”

“A sabida haka muka cika da mamaki, inda kawai da yammacin talata muka ga mutane sun zo sun hau ginin da katafila suna rushewa ba tare da sun bamu wani notis ba”

“Babu wani wanda ya kawo mana takarda ko ta tsire ce da sunan za’a rushe wannan gini, haka kurum muka ga sun fara kai ginin kasa” A cewar llauyan.

A lokacin da yake mayar da martani, Muktar Usamn, wanda Darakta ne mai kula da sashin birnin tarayya ta FCTA, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, cewar ginin ba shi da wani izni, kuma hukuma ta sanar a rubuce kafin ta rushe ginin.

Ya kara da cewar, ginin ba shi kadai ne hukumar ta rushe ba a unguwar da ginin yake, akwai sauran gine gine da dama da muka rushe.

Mista Mukhtar yace, jami’an hukumarsu da suke aikin rushe ginin anci zarafinsu sosai a lokacin da suke aikin rusau din a harabar ginin.

NAN

LEAVE A REPLY