Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya fada komar jami’an hukumar EFCC ta kasa.

Mai rikon mukamin mai magana da yawun hukumar, Samin Amaddin ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Sai dai kakakin rundunar yace Mista Babachir yana bayar da hadin kai a dukkan ambayoyin da ake yi masa.

Har ya zuwa wannan ranar ta Alhamis dai tsohon sakataren Gwamnatin yana hannun hukumar ta EFCC.

Hukumar dai ta kame tsohon sakataren Gwamnatin ne sabida zarginsa da akai da sama da fadi na kusan naira miliyan 200,kudin da aka ware domin yankan ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira.

Jami’an hukumar sun bayyana cewar akwai kwararrun jami’anta da suke binciken dukkan takardun da suka shafi wannan batu.

LEAVE A REPLY