Ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda Shugaba Muhammadu Buhari yake, abinda ya sanya firgici da kuma tsaro, kasancewar kwanansa biyu da baro kasar Amurka, bayan da yayi wata ganawa ta musamman da Shugaban Amurka Donald Trump.

A ranar Laraba da ta gabata dai aka yi tsammanin dawowar Shugaba Buhari zuwa gida Najeriya. Sai dai jirgin da yake dauke da Shugaba Buhari mai suna ‘eagle one’ ya bar filin jirgin saman ‘Joint Base Andrew na sojojin Amurka’ dake birnin Washington tun ranar Talata.

Sai dai kuma, anga saukar jirgin na Shugaban kasa a birnin Landan da misalin karfe 9:42 na dare a cewar na’urar da ke bibiyar jirgin na Shugaban kasa. Har ya zuwa yau ranar Alhamis, jirgin da yake dauke da Shugaban kasa yana birnin Landan.

A ranar 27 ga watan Afrilu, a sanarwar da fadar Shugaban kasa ta bayar dangane da ziyarar Shugaban kasa zuwa kasar Amurka, ta bayyana cewar zai bar najeriya ranar 28 ga watan Afrilu, sanarwar kuma bata bayyana cewar Shugaban zai tsaya a Landan ba.

Sanarwar tayi bayani ne kawai akan ziyarar da Shugaba Buhari zai kai kasar Amurka, da kuma bayanan abubuwan da zai yi a kasar ta Amurka da batun ganawarsa da Shugaba Donald Trump da kuma batun ganawarsa da manyan ‘yan kasuwar Amurka.

Shugaba Buhari ya isa birnin Washington a ranar 9 ga watan Afrilu, yayin da ya gana da Shugaba Donald Trump kuma suka yi wata ganawa ta musamman tare da kuma taron manema labarai da suka gudanar tare a fadar White House.

Haka kuma, a sanarwar da mai taimakawa Shugaban kasa a sabbin kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya rubuta cewar Shugaba Buhari ya baro kasar Amurka rnar 1 ga watan Mayu, inda bashir din ya bayyana cewar Shugaba Buhari yana kan hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja, Najeriya.

Babu dai wata sanarwa da fadar Shugaban kasa ta bayar dangane da sauyin inda Shugaba Buhari zashi, ko karin hasken dalilin da ya sanya aka ga saukar jirgin da yake dauke da shi a birnin Landan na kasar Burtaniya.

 

LEAVE A REPLY