Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II
Daga Hassan Y. A. Malik

Sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi na II ya bawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wasu shawarwari game da albashin ‘yan majalisun tarayyar kasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, sarki Sanusi ya shawarci shugaban da ya raba albashin ‘yan majalisun gida biyu ya yi amfani da rabi wajen daukan matasa aiki.

A cewar sarki Sanusi, idan aka raba albashin kowanne dan majalisa a Nijeriya, aka tara rabin guri guda, to, zai iya biyan ‘yan Nijeriya guda 70,400 albashi mai tsoka N90,000 zuwa N92,000 a kowanne wata.

A cewar sa, kowane sanata a Nijeriya na samun miliyan 36 a kowani wata, wanda idan aka raba biyu zai bada miliyan 18. Ya ce, tunda akwai sanatoci guda 109, idan aka tara wadannan kudi za su iya bawa ‘yan Nijeriya guda 21,800 aikin yi, inda rabin albashin kowanne sanata daya na wata guda zai dauki ‘yan Nijeriya 200 aiki.

Haka zalika. sarki Sanusi ya ce kowane dan majalisar wakilai na daukan miliyan 25 a kowane wata, wanda idan aka raba shi gida biyu za a samu Naira miliyan 12.5. Ya ce tunda akwai ‘yan majalisar wakilai 360, idan aka tara rabin albashin su gaba daya, za a iya samarwa ‘yan Nijeriya guda 48,600 aikin yi, inda rabin albashin kowane dayan su zai samar da ayyukan yi ga mutane 135 akan albashin N92,500 a kowane wata

Sarki Sanusi ya ci gaba da cewa, rabin albashin wadannan sanatoci ya ma yi masu yawa idan aka yi la’akari da cewar yawancin ‘yan Nijeriya ba sa kashe sama da dala daya a kowacce rana.

Haka zalika ya koka da yadda ake biyan sojojin Nijeirya Naira dubu 49,000 a kowanne wata duk da cewa suna sanya rayuwar su a cikin hatsari, inda wasu daga cikin su ko gurin zama ba a basu ba.

Ya yi kira ga shugaba Buhari da ya duba wannan lamari, da sauran ‘yan Nijeirya da su yada wannan batu ta yadda wadannan ‘yan majalisu za su san ‘yan Nijeriya guda nawa suka hana aikin yi saboda handamar su.

LEAVE A REPLY