Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewar hadin kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ne zai sa jama’a su sake amincewa jam’iyyar. Atikun ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a babban taron jam’iyyar da ya zabi sabbin Shugabannin da zasu ja ragamar jam’iyyar. Ga jawabin na Atiku Abubakar:

Duk tsawoncin rayuwa ta, ni mutum ne da yayi Imani da Kasarmu  Nijeriya. Nayi Imani da cewa Nijeriya zata iya zama kasa daya mai baiwa kowane dan kasa ko yar kasa damar yin fice ga al’amarinsa ba tare da banbanci ba.
Nayi Imani da cewar Najeriya tana iya zama kasa daya mai kudurin alheri ga dukkan dan kasa. Wannan Imani da nike dashine ya bani kwarin guiwar hada hannu da sauran ‘yan-uwana ‘yan Nijeriya masu irin wannan ra’ayi domin mu kafa Jam’iyyar Mutanen Damokradiyya (watau PDP) wadda mukayi wa ginshiki na hadin kan kasa, kuma muka gina ta a kan tafarkin zumunci, gaskiya, da kuma adalci ga ko wane dan kasa ba tare da bambanci ba.
Jamiyar PDP da muka gina, ta kafu ne a kan tafarkin damokradiya, kuma ta aminta da bin tsari irin na damokradiyaa cikin duk tsare-tsaren tafiyar da al’amurran yau da kullum na Jam’iyyar. Wannan manhaja itace kawai zata iya shimfida mulki na gaskiya da adalci a kasarmu Najeriya. Yin haka din shine tubalin ginin sahihiyar kasa mai haddin kai wadda dukkan ‘ya’yanta zasuyi alfahari da ita.
Wannan ya zama dole ne domin sai da hadin kai ne kawai zamu iya shinfida ginshikin tattalin arziki wanda zai haifar da ayyuka ya kuma ba kowane dan kasa damar yin fice a kowane zarafin rayuwa.
Tunda aka kafa Jam’iyyar nan ta PDP, shekaru goma sha tara (19) da suka wuce, imanina na nan daram dam akan wadannan ginshikoki da muka kafa wannan Jam’iyyar akansu, duk kuwa da yake akwai wadansumu da dama da suka rikide suka kuma chanza matsayinsu.
A cikin wadannan shekarun:
Nayi yaki da rabe-raben  kawunan ‘yan jam’iyarmu. Nayi yakin kare Tsarin Mulkin Jam’iyarmu da kuma tsarin Mulkin Kasarmu, Najeriya, wanda har ma yin haka din ya ja akayi amfanin da karfin mulki aka fiddani daga cikin Jam’iyyar da na taimaka aka kirkiro. Wannan kuwa bai bani mamakiba domin na daukeshi tamkar sakamako ne da mutum ka iya samu domin fafutukar dawwamar mulkin damokradiya a kasarmu.
Imani na akan tubalin da muka gina ginshikinJam’iyar PDP a kanshi baitaba girgizaba, a duk halin da na samu kaina. A yau dinnan ina nan zaune daram bisa kan wadannan ginshikokin, kamar yadda na zauna a kansu ranar 17 ga watan Agusta, 1988, lokacin da Marigayi Alex Ekwume, da Marigayi Solomom Lar, da Marigayi Abubakar Rimi da sauran manya manyan yan kishin kasa da suka hadu suka sanar wa duniya da haihuwar Jam’iyar PDP.
A yau dinnan, ina alfaharin shaida maku cewar na dawo gida. Na dawo Jam’iyarmu.
Ina chike da farin ciki da kuma alfaharin cewar Jam’iyar nan tamu ta PDP itace ta samu nasarar kwace mulki daga hannu sojoji a shekarar 1999
Ina kuma cike da farin ciki da alfahari cewar Jam’iyar mu ta PDP itace daya tilo wadda ta kawo damar da zababben shugaban kasa ya kare mulkinsa ya kuma mika jagorancin kasar zuwa ga wani sabon zababben shugaban kasa a cikin shekarar 2007.
Ina alfahari da cewar a cikin shekarar 2015, wannan Jam’iyyar ta PDP ta jagoranci zaben da ya mika mulki zuwa ga dan takarar shugaban kasa daga Jam’iyyar adawa lami lafiya.
Ina kuma matukar alfahari da cewa gwamnatin Jam’iyar PDP ta kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da ba’a taba samun irinsa ba a tarihin Najeriya.
Amma kash! A cikin shekarar 2015, Jam’iyyar PDP bata da hadin kai, ta wargaje. A saboda hakane kuma, mutanen Najeriya suka juya mata baya suka zabi chanji.
Anyi wa ‘yan Najeriya alkawarin yalwatar arziki, da zaman lafiya da kuma mulkin gaskiya ba boye-boyen komai.
Ashe abin duk yaudara ce.
Jam’iyyar APC ta yi alkawarin kirkiro ayyuka milyan ukku a kowace shekara. Amma sai gata tana rusa ayyuka milyan ukku a kowace shekara.
Jam’iyyar APC tayi mana alkawarin zaman lafiya da kuma hadin kan yan kasa baki daya. Amma sai gashi kasarmu, a yau, ta samu rarrabuwa da kuma rashin kishi da hadin kan junan da bata taba samu ba tun lokacin da aka gama yakin basasa a Najeriya.
Jam’iyyar APC tayi alkawarin sake shirin jihohin Najeriya domin qyara yanayin zaman Jamhuriyarmu. Amma da ta dare bisakan gadon mulki, sai ta juya wa shirin baya, tayi watsi da shi.
Jam’iyyar APC tayi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa. Amman babu yakin da suka sa a gabansu yanzu banda fataucin yan adawa. “Suna ba albasa ruwa amma kuma suna tuge tumatari.”
A Najeriyar mu a yau, idan kai dan jam’iyar adawa ne, kuma aka tsinkayi cewar zaka iya razana jam’iyar gwamnati, sai a fara kama yaranka da abokan huddarka a daure, a kuma fara muzguna ma Kampanonin kasuwancinka.
Duk da manyan kurakuaran da gwamnatinmu ta PDP ta yi lokacin da ta ke kam mulki, yau mutanen kasarmu na juyayin wucewar gwanmatin. Sukan ce “jiya ba yau ba ………”
Kuma suna fadan haka din da kyakkyawar hujja: domin lokacin da Jam’iyar PDP to karbi mulkin Nigeria a shekarar 1999:
Yawa-yawan yan Najeriya basa wuce shekara 44 a duniya sai su mutu.
A duk fadin Najeriya ba za’a iya alfahari da wayoyin tarho na hannu da suka kai milyan daya ba.
Tattalin Arzikin kasarmu shine na ukku mafi karfi a nahiyar Africa.
Bayan shekaru goma sha shidda (16) da jam’iyar PDP ta shugabanci gwamnatin kasarmu, da ta sauka daga karagar mulki  a cikin shekarar 2015, ta bar Najeriaya a cikin wani sabon yanayi kamar haka:
Ta kara shekaru goma (10) akan adadin yawan shekarun da mafi yawan yan Najeriya sukeyi a duniya kafin su mutum. Watau yanzu shekarun sun zama hamsin da hudu (54)
Ta baiwa ‘yan Najeriya milyan chasain da tara (99 million)  damar amfani da wayar salula.
Ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya har ya zama na daya a cikin Africa, ya wuce na Masar (Egypt) da kuma Africa ta Kudu (South Africa).
Ni kanyi matukar mamaki da juyayi a duk lokacin da naji ana maganar cewar tabarbarewar farashin man petur shine dalilin da yasa gwamnatinmu take gazawa.
A yau din nan, farashin gangar Man Petur bai taba sauka kasa da dala Amirka hamsin ($50) ba. Amma zamanin da na zama mataimakin shugaban kasar Najeriya, farashin gangar man petur bai wuce dala amirka ashirin ($20) ba.
Na taka rawar gani wajen samowa da kuma daukar hazikan yan kasa masu ilimin tattalin arziki wadanda suka taimaka ainun wajen habbaka tattalin arzikin kasarmu da kashi kamar shidda cikin dari (6%) a kowace shekara.
Babban abin burgewa ma a nan shine, sai gashi mun yi amfani da dan kudaden da muke samu mun biya duk basukan da ake bin kasarmu daga kasashen waje.
Wannan shine ya gwada mana cewar yadda kasa tayi amfani da arzikin ta ya fi muhimmanci fiye da adadin ma’adinan da take da su.
A matsayinmu na ‘ya’yan jam’iyar PDP muna da abubuwan yin alfahari da yawa. A cikin shekarun nan goma sha shidda (16) da mukayi muna mulki a najeriya, mun sami zaman lafiya da habakar arzikin kasa mai tarin yawa.
Babu shakka munyi wasu kurakurai, amma bamuyi watsi da hadin kan kasa ba.
Bamu maida jihohin da suka zabemu ba ‘ya’yan bora muka kuma maida jihohin da basu zabe mu ba ‘ya’yan mowa.
Amma kash! Sai gashi yanzu muna karkashin mulki Jam’iyar APC wadda ta share fiye da shekaru biyu kan mulki amma har yanzu tana kuka da gwamnatin da ta gada a kan tabarbarewar al’amurran ta, tana kuka da jama’a maimakon share masu hawaye, domin share masu hawayen nan shine musabbabin da yasa aka zabesu.
Jam’iyar PDP itace zata kyautats tsarin shirin Jamhuriyar Najeriya, ta inganta ma’aikatunta, ta kuma mika mulki zuwa ga hannun talakawa. Kuma zata yi hakan ne ta hanyar:
Karfafa Masana-antu da hada-hadar kasuwanci wanda zai kirkiro ayyukan yi irin wadanda gwamnati bazata iya yi ba;
Za ta kafa tsarin tattalin arzikin kasa na ‘yan “Jari-Hujja” wanda zai karfafa wa jama’a gyuiwar saka jari domin kirkiro ayyukan yi a kasa.
Zata gyara yanayin Gwamnati domin ta zamo ingantacciya mai kuzari da kuma sanin ya kamata. Gwamnatin PDP ba zata yarda ta dauki kaso mafi tsoka na  kasafin kudi domin biyan albashin ma’aikatan gwamnatin da ba su shige kashi daya cikin dari (1%)na jama’ar kasar ba.
Duk da matsalolin da Jam’iyar PDP take ciki a halin yanzu, itace jamiyar da tafi bazuwa a kowane bangare da sashe na Najeriya. Dole ne mu sake salon tafiya domin ‘yan Najeriya su aminta da mu su sake maidamu a bisa karagar mulki. Idan har Allah ya sake bamu mulki, to dole ne muyi aiki tukuru domin daukaka martabar kasarmu najeriya da kuma dawwamar da mulki demokradiya a cikin ta.
Ba zamu iya yin haka ba sai idan munyi aiki da kuduri guda cikin hadin kai. Ainihin hadin kanmu shine babban tubalin ginin mafificiyar kasa mai adalci ga jamaarta. Dole ne mu manta da yin mummunan zargi ga junanmu, kuma mu zage damtse domin baiwa duk dan najeriay damar shahara akan aikinsa ba tare da la’akari da jinsinsa ba ko kuma addininsa.
Dole mu kasance Jam’iyar da take kawo kyakkyawan tsarukan da zasu baiwa duk yan kasarmu kwazo da karfin gyuiwar dogaro da kuma alfahari da kasarsu Najeriya, ba wai kawai su so su labe wajen kauyukansu ba ko kuma cikin kabilun su kawai ba. Ko kuma ma sufi shaawar barin kasar dun-gurun-gun.
Hakkinmu ne da kai da kuma ni mu tabbatar cewarmun zamanto Jam’iyar da zata kawo waraka a cikin kasarmu ba Baraka ba. Zamu tabbatar cewa ba za’a sake rarraba kawunanmu ba har abada.
Saboda haka, a wannan dandalin babban taron Jam’iyar nan tamu, dole ne mu tabbatar da cewa mun zabi shugabannin Jam’iya masu basira da kwakwalwa, wadanda suke da hangen nesa kuma suna da kudurin daukaka kasarsu fiye da misali. Shugabannin da suka fahimci bukatar aiki cikin gaggawa domin ci gaban kasarmu Najeriya.
Ya kamata ku zabi shugabannin da suka gwanance wajen ginin Jam’iya domin su taimaki PDP ta zama amintacciyar Jam’iya wadda ta bambanta da Jam’iyar “Kama-Karya” ta APC.
Mu zabi shugabannin da basu da wata yana a cikin idanunsu wadda zata hana su ganin cewar zamanin nan namu ya canza kuma guguwar chanjin nan bazata bar duk wadanda ba zai fahimci sabuwar alkiblar ba. Misali, muna bukatar shugabannin da suka fahimci cewar kasuwar man petur a cikin duniyar makamashi ta na dushewa kuma dushewarnan zata saka kasarmu cikin mummunar damuwa idan ba mu chanza ba cikin sauri.
Wallahi muna bukatar shugabannin da suka fahimci hikimar  gyaran shirin zamantakewa da kuma tsarin tattalin arzikin kasarmu ta yadda za’a bar gwamnatocin jihohi su taka gagarumar rawa cikin ayyukan ci gaban kasa, wadanda kuma zasu iya janye ragamar tattalin arzikin kasarmu daga man petur, su kuma hana korafe-korafen wariyar al-umma da takura wa kananan kabilu. Wadannan sune shugabannin da zasu karfafa zamantakewarmu su kuma gina kasarmu da kyau.

 

LEAVE A REPLY