gwamnonin jam’iyyar  APC guda 24 sun marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya kan dakatar da wa’adin Shugaban jam’iyyar na kasa John Oyegun, a cewarsu dole Oyegun ya bar ofis sabida karewar wa’adin Shugabancinsa.

JaridarDAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar a ranar 27 ga watan maris, Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, inda yace wa’adin mulkin Oyegun ya kare, dole ya sauka daga mukaminsa na Shugaban jam’iyyar.

Bola Tinubu, wanda shi ne jagoran kwamitin da yake sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar  da ba sa ga maciji da juna, tuni ta bayyana ana sa-toka sa-katse tsakaninsa da Shugaban jam’iyyar John Oyegun.

A ranar Talata, Gwamnonin jam’iyya mai mulki suka yi wata ganawa ta musamman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Gwamnati dake Aso Villa a Abuja, inda daga karshe aka kare taron dutse hannun riga, Gwamnonin suka rabu gida biyu kan Shugabancin jam’iyyar na kasa.

Sai dai kuma,daga bisani, Shugaban Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, a ranar Laraba ya shaidawa manema labarai cewar an kawo karshen dukkan wata turka turka kan batun wa’adin Shugabancin Oyegun, inda yace Gwamnonin sun goyin bayan matsayar Shugaba Buhari kan wannan batu.

A lokacin da yake magana da ‘yan jarida dake fadar  Shugaban kasa, bayan ya gana da Shugaba Buhari tare da wasu gwamnoni, Gwamna Yari, ya bayyana cewar a halinsu yanzu Gwamnonin na tare da matsayar Shugaba buhari kan wa’adin Shugabancin Oyegun, bayan da suka tattauna a tsakaninsu.

“Bayan mun tattauna da juna, dukkan gwamnoni 24 na APC suna tare da matsayar Shugaban kasa, a saboda haka zamu mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, sannan kuma zamu mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya”

“A dangane da haka, dukkanmu mun amince cewar za’a yi ‘yar tinke a dukkan mazabu da kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya domin zaben sabbin Shugabanni” A cewar Gwamna Yari.

LEAVE A REPLY