Kungiyar Gwamnonin Najeriya da aka fi sani da ‘Governors Forum’ a ranar Laraba ta hadu a babban birnin tarayya Abuja, domin tattaunawa kan batun da ya shafi mafi karancin albashi da shanin tabarbarewar tsaro a Najeriya da sauran batutuwa.

Haka kuma,kungiyar kwadago ta Najeriya na neman a mayar da mafi karancin albashi ya koma Naira dubu sittin da biyar ga kowanne ma’aikaci, inda suke neman lallai Gwamnonin su amincewa da wannan a matsayin albashi mafi karanci a Najeriya.

A wajen taron kuma, an sanya kudurin tattauna batun halin rashin zaman lafiya da ake fama da shi a kasarnan musamman Jos babban birnin jihaar Filato.

Bayan haka kuma,ana sa ran Gwamonin zasu gana da Antoni janar na jihohin kasarnan 36 tare da Shugaban hukumar aikewa da sakwanni ta Najeriya domin tattauna batun harajin aika sako.

Sannan kuma ana sa ran Gwamonin zasu tattauna akan sabatta juyatta da ake yi tsakanin bangaren zartarwa da kuma bangaren majalisun dokokin tarayya.

Haka kuma, ana sa ran babban kamfanin mai na kasa NNPC zai gabatar da jawabi a taron Gwamnonin domin bayyana musu hakikanin kudaden da ake samu daga cinikin mai da kuma harajin da ake biya.

 

LEAVE A REPLY