Ministan harkokin kimiyya da fasa na Najeriya, Ogbonnaya Onu, ya bayyana cewar, na’urorin zabe masu amfani da hasken rana wadan da hukumar kula da kere-keren kimiyya ta kasa NASENI ta samar sun gama kammaluwa domin amfani da su a wannan zabe mai zuwa.

Mista Inu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja a lokacin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labbarai na Najeriya NAN.

A cewarsa, wadannan kayayyaki, sun dace da tsarin dukkan kasashen duniya, domin anyisu da inganci domin zabe ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa.

Yace,amfani da wadannan kayayyakin zaben ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa, zai yuwu ne idan har hukumar zab ta kasa ta amince da su kuma ta gamsu ayi amfani da su a zaben 2019 ko 2023.

“Mun inganta na’urorinmu masu amfani da hasken rana domin zaben nan,kuma tuni muka gabatarwa da hukumar zabe ta kasa wadannan kayayyaki. Kuma hukumar zaben ta gamsu da ingancin kayayyakin”

“Haka kuma, mun gabatar da wadannan kayayyakin zabe ga babban kwamitin kula da tattalin arziki na kasa wanda mataimakin Shugaban kasa yake shugabanta tare da Gwamnoni a matsayain mambobi duk mun nuna musu wadannan kayan zabe masu amfani da hasken rana”

“Amma mu ba zamu iya cewar za’a yi amfani da wadannan kayan zabe a wannan zaben da yake tafe ba na 2019 ko 2023, wannan hukumar zabe ta kasa INEC ce ke da wannan ikon”

Mista Inu ya kara da cewar, makasudin wannan muhimmin aiki shi ne, inganta harkar amfani da kayayyaki masu amfani da hasken rana a yayin zabubbuka domin tattara sakamakon zabe cikin sauki da kuma yin zabe cikin gaskiya da adalci.

Ministan ya cigaba da cewar, kayayyakin zaben zasu taimaka wajen tattara sakamakon zabe cikin lokaci ba tare da wani jinkiri ba, haka kuma, ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje suma zasu iya yin zabe ta wannan hanya cikin sauki.

Yace, an samar da wadannan kayayyakin zabe masu amfani da hasken rana bisa sahalewar hukumar zabe ta kasa INEC.

“Wannan hoton shi ne samfurin na’urar da Ministan harkokin imiyya da fasa ya gabatar”
A wani cigaban kuma, Ministan ya bayyana cewar, Najeriya na tattaunawa da wasu kasashe domin samarwa da kasar na’urar tauraron dan adam ta musamman.
“A sabida haka, a madadin kasa daya ta mallaki na’urar tauraron dan adam ita kadai yanzu kasashe da yawa zasu iya mallaka kuma su yi amfani da su”

 

LEAVE A REPLY