Hoton 'yan matan Makarantar Dapchi wanda The Nation ta dauka

Gwamnati tarayya Najeriya a ranarLahadi ta tabbatar da sace ‘yan matan Makarantar Gwamnati dake Dapchi a jihar Yobe, a sakamakon wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kaiwa makarantar a ranar litinin din da ta gabata.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Damaturu bayan da yayi wata ganawar sirri tsakanin wakilan Gwamnatin tarayya da Gwamnatin jihar Yobe da kuma jami’an tsaro da kuma dangin ‘yan matan da aka sace.

“Tattaunawa ce da aka yita tsakanin masu ruwa da tsaki, domin samun sahihan bayanai akan adadin ‘yan matan da aka sace, bayanai sun nuna cewar ‘yan mata 906 aka sace,amma hakinanin wadan da aka sace sune 110”

Ministan ya bayyana cewar, daga cikin abubuwan da suka cimma a yayin wannan tattaunawa, sun hada da tura karin jami’an tsaron ‘yan sanda da kuma jami’an NSCDC zuwa makarantar Dapchi.

Ya kara da cewar, dukkan jami’an tsaro suna yin aiki tukuru domin tabbatar da an kwato wadannan ‘yan mata daga hannun wadan da suka sace su.

“Zamu yi duk abinda ya dace wajen ganin mun tabbatar da kubutar wadannan ‘yan mata” A lokacin da Ministan yake bayar da tabbaci.

Ya bayyana cewar, Gwamnatin tarayya tare da Gwamnatin jihar Yobe da kuma hadin guiwar iyayen wadannan ‘yan mata zasu yi aiki tare domin tabbatar da kubutar wadannan ‘yan mata lami lafiya ba tare da sun cutu ba.

Alhaji Lai Mohammed, ya jaddada cewar, lallai gwamnati ta ci lagon ‘yan ta’adda shi yasa suke neman wasu hanyoyi da suke son nuna lallai suna nan, amma dai an ci galaba kansu.

“”Gwamnati zata cigaba da rubanya kokari wajen yaki da ‘yan ta’adda, sannan zata kuma tabbatar an  kubutar da wadannan ‘yan mata da aka sace, tare da duk wani dan Najeriya dake hannunsu”

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ta ruwaito cewar, ‘yan ta’adda sun kaiwa Makarantar Gwamnati ta ‘yan mata dake Dapchi hari a ranar litinin din da ta gabata, inda aka sace wasu daga cikinsu.

NAN

LEAVE A REPLY