Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

A ranar Alhamis Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aiwatar da wasu sauye sauye a majalisar zartarwar jihar. Hakan ya biyo bayan nada Albdullahi Abbas a matsayin Kwamishina da aka yi ne, Abdullahi Abbas ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, inda nan take majalisar dokokin Kano ta amince da shi a matsayin kwamishina.

Bayan da Gwamnan ya rantsar da shi, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya turashi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman, yayin da Musa Iliyasu Kwankwaso dake zaman kwamishina a ma’aikatar aka tura shi zuwa, raya karkara.

A lokacin da yake bayar da sanarwar wadannan sauye sauye, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yace wadannan sauye sauye suna cikin tanade tanaden Gwamnatinsa domin sabunta yanayin aikin kwamishinoninsa, da kuma horar da su aiki tukuru.

Bayan haka kuma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da Injiniya Bashir Karaye a matsayin sabon Shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar Kano, bayan da Abdullahi Abbas yayi murabus daga mukaminsa.

Gwamnan yace, wasikar da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta aikowa reshen jihar Kano na jam’iyyar shi ne ya kawo karshen takaddamar da ake yi akan batun shugabancin jam’iyyar na jihar kano.

LEAVE A REPLY