Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Bayan murabus din mataimakin Gwamnan Kano farfesa Hafizu Abubakar  a jiya Lahadi, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na neman wanda zai maye gurbin Hafizu.

Tuni dai ake ta rade radi kan mutane biyar wanda suka hada da Hon Suleman Abdulrahman Kawu Sumaila mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar wakilai.

Sai Nasiru Yusuf Gawuna wanda shi ne kwamishinan harkar gona na Gwamnatin Gandujen, wanda ya nuna aniyarsa ta neman wannan mukamin.

Mutum shi ne kwamishinan harkokin yada labarai matasa da wasanni Malam Muhammad Garba, wanda shima ake yiwa kallon na kusa da Gwamna Ganduje wanda ana iya daukarsa domin zaman sabon mataimakin Gwamnan Kano.

Muratala Sule Garo shi ne mutum na hadu da ake masa kallon yana da alaka ta kut da kut da Gwamna Ganduje, wanda kuma shi ne kwamishina a ma’aikatar harkokin kananan hukumomi, sai dai kuma yaa fito ne daga karamar hukumar Kabo a yankin Kano ta Arewa wanda yankin da Gwamna Ganduje ya fito kenan.

Mutum na biyar shi ne Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas. shi dai Abdullahi Abbas ya fito ne daga yankin karamar hukumar Gwale karamar hukumar  da tsohon mataimakin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar ya fito, ana kuma kallon cewar Gwamnan na iya mayarda kujerar mataimakinsa zuwa karamar hukumarta Gwale.

LEAVE A REPLY