Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP mai adawa.

Gwamnan ya bayar da wannan sanarwa ne a ranar Laraba 25 ga watan Yuli 2018 a gidan gwamnatin jihar dake birnin Makurdi.

Daraktan yada labarai na Gwamnan jihar Terve Akase ya kara da cewar Gwamnan ya yanke wannan shawara ne yayin da al’ummar jihar suka nemi yayi hakan.

Tun da sanyin safiyar ranar Laraba ne dubun dubatar matasan jihar Binuwai suka tarewa Gwamnan hanya domin hana shi halartar babban taron jam’iyyarvAPC da ya shirya halarta a yau a babban birnin tarayya Abuja.

Tun da misalin karfe 8 na safe ne matasan suka mamaye gidan Gwamnatin jihar,inda suka toshe dukkan wata hanya da Gwamnan zai fito domin halartar taeron jam’iyyar APC a Abuja.

A lokacin da Gwamnan ya fito domin tafiya Abuja, tuni matasan suka haro katangar gidan Gwamnatin, inda suka tare motar Gwamnan, abinda ya janyo dole Gwamnan ya tsaya domin sauraren matasan.

A cewar wata majiya, GWamnan yayi nufin tafiya Abuja domin halartar taron da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta kira domin sasanta sabain dake tsakaninsa da tsohon Gwamnan jihar George Akume.

Matasan da suka yiwa gidan Gwamnatin tsinke sun rike kwalaye dauke da rubuce rubuce iri iri, wasu na cewa”Ortom kada ka koma APC” wasu kuma na cewar “Ortom dole ka fice daga APC”.

LEAVE A REPLY