Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom

Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom yana yin kwangaba kwam-baya kan batun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Bayan da Gwamnan ya bayyana cewar zai fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.Shugabannin jam’iyyar APC sun zauna da shi inda ya tabbatar musu da cewar yana nan daram dam dam a cikin jam’iyyar  ta APC.

Sai dai kuma ‘yan awanni bayan sun yi wannan tattanawa da Shugabannin jam’iyyar APC na kasa, Gwamnan ya kuma canza baki, inda ya bayyana cewar babu dalilin da zai hana shi ficewa daga cikin jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY