Wata gobara da ta tashi a tsakiyar daren jiya ta kone babbar kasuwar ‘Terminus’ dake tsakiyar garin Jos a jihar Filato.

Gobarar dai ta yi barna da yawa a yadda wani da ya ganewa idonsa ya shaidawa majiyarmu.

Tun farkon tashin gobarar dai jami’an kwana kwana suka yi kokarin kashe ta, kafin daga bisani su ci nasarar kashe ta bayan tayi gagarumar barna.

Wani ganau ya shaida mana cewar galibi gobarar ta fi yiwa ‘yan tebur tebur barna, sannan kuma ta ci shaguna da yawa a cikin kasuwar.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai ba san musabbabiyar faruwar wannan gobara ba. Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato ya tabbatar da aukuwar wannan gobara.

 

LEAVE A REPLY