Gwamnatin jihar Borno, ta bayyana cewar gidan tsohon Shugaban kungiyar Boko Haram, Muhammad Yusuf zai koma gidan tarihi da al’adu a birnin Maiduguri.

Kamishinan yada labarai da al’adu na jihar Mohammed Bulama ne ya bayyana hakan, a babban taron makon al’adun gargajiya da wasanni na Najeriya da ake gudanarwa a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Kamfanin dillanci labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar taken taron na bana shi ne “Amfani da kayan tarihi domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya” taron wadda Ma’aikatar yada labarai da al’adu ta kasa karkashin jagorancin Lai Mohammed ta shirya.

Bulama ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Najeriya cewar, za’a mayar da gidan tsohon jagoran kungiyar ya koma gidan tarihi ne, domin adana dukkan wasu bayanai da suke da alaka da al’amarin na Boko Haram a jihar, domin amfanin mutanan baya.

“Zamu mayar da gidan jagoran kungiyar na farko ya koma gidan tarihi domin amfanin wadan da zasu zo a baya su san ainihin abinda ya faru, domin kuwa Boko Haram ta samo asali ne daga gidan jagoran kungiyar na farko Muhammad Yusuf”

“Ana kiran gidan Jagoran kungiyar na farko Markaz, amma zamu canja shi zuwa gidan adana kayan tarihi da al’adu, amma zai kunshi kadai abinda yake da alaka da Boko Haram ne”

Shi dai jagoran kungiyar na farko Muhammad Yusuf, an kashe shi ne a 2009 abinda ya fusata ‘ya ‘yan kungiyar suka shiga tayar da kayar baya babu kakkautawa tun bayan kisan shugaban nasu a jihar Borno da wasu yankuna na yankin Arewa maso gabas.

HHaka kuma,Kwamashinan ya kara da cewar, Gwamnatin jihar Borno na tunanin mayar da dajin Sambisa ya zama wani sansanin shakatawa da yawon bude ido domin jan hankalin baki ‘yan yawon shakatawa.

 

 

LEAVE A REPLY