Kanar Hameed Ali

Babban shugaban hukumar kwastan ta  ƙasa kanar Hameed Ali mai ritaya ya zargi Shugaba Buhari da cewar kusan rabin masu riƙe da muƙamai a gwamnatin ‘yan PDP ne. Yace gwamnatin bata tafiya yadda ya dace, domin ta biyawa ‘yan Najeriya aalkawuran da ta dauka musu yayin yakin neman zabe.

Yace, galibi mutanan da suke tare da Shugaba Buhari ba su yi amnanna da irin manufofinsa da salon mulkinsa ba, illa kawai yunkurinsu na karasa gurgu da taɗiya. Yace sam abn da yake tafiya yanzu a gwamnatin ba haka ya dace ace Gwamnatin na tafiyar da su ba.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, shima ya goyi bayan wannan magana ta kanar Hameed Ali, inda yace, su a matsayinsu na Gwamnoni an jingine su wajen naɗe-naɗen mukai a wannan Gwamnati.

Kanar Hameed Ali mai eitaya yana magana ne, a jiya yayin kaddamar da sabon ofishin yakin neman sake zaben Shugaba Buhari a matsayin Shugaban kasa a shekarar 2019 a Abuja babban birnin tarayya.

Yace, “ba muda wata tantama akan nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma dai akwai mutanan da suka wahaltawa wannan tafiya tun farko, amman yanzu anyi wancakali da su, an debo ‘ya ‘yan mage”

“Ina tabbatar muku da cewar, wadannan tsintattun mutanen da suka mamaye wannan Gwamnatin sune suka fi kowa karfin fada aji a cikinta, alhali wadan da suka sha wahalarta har ta kafu sun zama ‘yan kallo”.

“Ba zamu taba zuba idanu ba, muna ji muna kallo mu bar wasu tsirarun mutane suna yin yadda sukaa ga dama, a wannan gwamnati, zamu tashi haikan, domin ganin abubuwa suna tafiya yadda ya kamata ace sun tafi”.

“Idan bamu tashi tsaye wajen kawo gyara a wannan gwamnatin ba, to zamu ji kunya wajen jama’armu, domin mune muka shiga lungu da sako muna kiran mutane su zabi wannan gwamnati domin yi musu abin da ya dace”

“Kuna zaton zamu koma, mu kalli ‘yan Najeriya mu ce musu mun gaza? Ko kusa, yanzu ne lokacin da zamu tashi domin kawo gyara mai ma’ana a wannan gwamnati da muka yi gumoi wajen kafata”

“Ko a lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, idan an fita Jihadi an dawo, ganimar da aka samo, ana rabata ne ga wadan da suka dauki makami suka yi yaki, ba wasu da suke kwance a gida ake rabawa ba”.

“A yau da nake magana da ku, a gwamnatin da muka kafa, muna da fiye da rabin masu rike da madafun iko duk ‘yan PDP da muka yaka ne a baya, taya zamu iya samun cigaba muna dauke da jibadau kayaan nauyi irin wannan?”

Kanar Hameed Ibrahim Ali dai yayi dogon jawabi a yayin bude wannan ofishi wanda za’a mika ragamar tafiyar da shi zuwa ga kungiyar magoya bayan Buhari ta BSO. A lokacin da yake yin nasa jawabin, Gwamnan jihar Filato Simon Baako Lalong, shima ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar yana yin nade nade a gwamnatinsa ba tare da ya tuntube su aba a matsayinsu na gwamnoni.

Yace tilas ne Shugaba kasa ya tashi domin kawo sauyin da ya yiwa ‘yan najeriya alkawari a yayin da ake yakin neman zabe, ba zai yuwu a cigaba da tafiya a irin wannan yanayi ba, har zuwa zabe mai zuwa.

Ko me zaku ce akan wannan bayanai da mutanan da suka kafa wannan Gwamnati suke yi?

LEAVE A REPLY